สรุปเนื้อหาตอนนี้
Yayin da wasu daga cikin ƴantakarar neman shugabancin Najeriya ke bayyana yiyuwar sake dawo da tsarin biyan tallafin man fetur matukar suka yi nasarar lashe zaɓen shekara mai zuwa, a nasa ɓangare Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa ka da a kuskura a dawo da wannan tallafi. IMF ya bayyana cewa duk wani yunkurin sake dawo da tallafin, zai kasance mummunan koma-baya a maimakon cigaba ga Najeriya. Shin me ye ra’ayoyinku a game da wannan kashedi da ya fito daga Asusun IMF zuwa ga ƴansiyasar Najeriya? Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...

ตอนต่าง ๆ
Ra'ayoyi kan gargaɗin IMF cewa kada a kuskura a dawo da tallafin mai a Najeriya
ฟังแล้วYayin da wasu daga cikin ƴantakarar neman shugabancin Najeriya ke bayyana yiyuwar sake dawo da tsarin biyan tallafin man fetur matukar suka yi nasarar lashe zaɓen shekara mai zuwa, a nasa ɓangare Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya yi gargaɗin cewa ka da a kuskura a dawo da wannan tallafi. IMF ya bayyana cewa duk wani yunkurin sake dawo da tallafin, zai kasance mummunan koma-baya a maimakon cigaba ga Najeriya. Shin me ye ra’ayoyinku a game da wannan kashedi da ya fito daga Asusun IMF zuwa ga ƴansiyasar Najeriya? Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyi mabanbanta...
Ra'ayoyi: Cikar Najeriya shekaru 10 ba tare da zartas da hukuncin kisa ba
ฟังแล้วA Najeriya an cika shekaru goma cur ba tare da an aiwatar da hukuncin kisa ba wanda ya samu sahakewar gwamnati, wadda ita kaɗai ce take ɗaukar matakin ƙarshen wajen aiwatar da hukuncin da kotuna suka yanke dangane da haka. Wannan dai lamari ne da ya sake biijoro da kiraye-kirayen ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da ke neman a samar da doka da za ta dakatar da aiwatar da hukunci a Najeriya.
Ra'ayoyin masu sauraro kan jingine shirin ƙara kuɗin mai a Nijar
ฟังแล้วMahukuntan Jamhuriyar Nijar sun jingine batun ƙara farashin mai duk da cewa Majalisar Dokokin Riƙon Kwaryar ƙasar ta bayar da shawarar yin wannan ƙari don magance ƙaracin makamashi da ake fama da shi a ƙasar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shirin rage farashin mai a tsawon wata ɗaya domin sauwaƙa wa jama’a. Latsa alamar sauti don sauraren ra'ayoyin jama'a...
Ra'ayoyin masu saurare kan kawo ƙarshen wasa da Argentina da Messi yayi
ฟังแล้วRa'ayoyin masu saurare kan wasan ƙarshe da Ɗan wasa Lionel Messi ya bugawa ƙasarsa. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Kabiru Muhammad Dan Bauchi.
Ra'ayoyin masu saurare kan fatan ci gaba da haƙo man fetur a wasu sassan arewacin Najeriya
ฟังแล้วTaron gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya da ya gudana a ƙarshen mako, ya buƙaci gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta farfaɗo da aikin binciken man fetur da aka faro tsawon shekaru a yankin. Kazalika taron ya buƙaci gwamnatin da ta mayar da hankali wajen gyara layin dogon da ya haɗa biranen Port-court-Jos-Bauchi-Gombe zuwa Maiduguri saboda muhimmancinsa wajen buƙasa tattalin arzikin al’ummar yankin. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.